Wednesday, 13 March 2019

Sun Sha Alwashin Yin Tattaki Daga Minna Zuwa Abuja A Kafa Saboda Murnar Cin Zaben Buhari

Wasu matasa biyu kenan da suka fara tattaki daga birnin Minna zuwa Abuja babban birnin tarayya domin nuna murnar su akan nasarar da shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello sukayi a zaben da ya gabata.


Matasan masu suna Mustapha da Musa tun kafin zabe sun sha alwashin da zarar shugabannin biyu sukayi nasara zasu taka da kafa daga Minna zuwa Abuja.

A halin yanzu suna hanyar Minna zuwa Abuja inda suke samun kyakkyawan tarba daga mutanen dake kauyukan hanyar.

Hausawa dai na fadin sakai yafi bauta ciwo.

Rariya.


No comments:

Post a Comment