Sunday, 31 March 2019

Ta kachame tsakanin mutanen Atiku akan zaben shugaban kasar da ya gabata

Rahotannin dake fitowa daga bangaren dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar na cewa ana can ana cece-kuce tsakanin mutanen Atikun kan yanda zaben shugaban kasar da ya gabata ya kasance da kuma yanda wasu jigogi a jam'iyyar suka yaudari Atikun.Jaridar TheNation tace ta samu labarin cewa mutanen Atikun na kallon tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da cewa basu taimakawa Atikun ba a zaben shugaban kasar da ya gabata, lura da yawan kuri'un da ya samu daga wadannan jihohi biyu.

Mutanen Atikun sun fahimci cewa dalilin Kwankwaso da Tambuwal na kin taimakawa Atiku a jihohin nasu shine suma suna da burikan zama shugaban kasa, sannan zasu so shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kammala mulkinshi na shekara takwas ya tafi, saboda irin goyon bayan da yake dashi zai iya basu barazana wajan cimma burinsu.

Sannan idan kuwa suka taimakawa Atiku yaci zabe, to zasu koma 'yan kallone a mulkin na Atiku.

Mutanen Atikun sun kara kulewa bayan da aka yi zaben gwamnoni suka ga cewa kuri'un da PDP ta samu a jihohin biyu, Kano da Sakkwato sun ninninka wanda ta samu a zaben shugaban kasa.

Akwai alamu masu karfi dake nuna cewa a zaben 2023 ma PDP dan Arewa zata tsayar a matsayin dan takarar shugaban kasarta.

No comments:

Post a Comment