Tuesday, 19 March 2019

TSAKANI DA ALLAH BA A KYAUTAWA ALARAMMA AHMAD SULAIMAN BA KUMA BA A RUFA MASA ASIRI BA

Na saurari audio har guda biyu wanda ake magana da mutanen da suka yi garkuwa da Sheikh Ahmad Suleman Kano, na farko sako ne Kidnappers din suke isarwa zuwa ga 'yan uwan Sheikh Ahmad suleman Kano.


Sannan audio na biyu maganar da shi Malam Ahmad Suleman Kano ya yi da Malam Nasir Salihu Gwandu ne a inda yake tsare a hannun masu garkuwa da shi.

Har ga Allah duk wanda ya saurari audio zai fahimci ba'a yiwa Malam Ahmad adalci ba da aka fitar da audion, kuma ba'a rufa masa asiri ba ko kadan, Malam yayi magana cikin yanayi da yake bayyana tashin hankali ga duk zuciyar da take cike da imani.

Fitar da audion bai dace ba sam, ba a kyauta ba! Ba a kyauta ba!! Ba'a kyauta ba!!! Kuma ba'a rufawa Malam asiri ba!!!

Ina kira ga shugaban kungiyar Izala na Kasa Ash-sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau da ya dauki matakin gaggawa na hana fitar da audio makamancin wannan, sannan kuma inda hali ya dace ayi diverting kiran waya na mutanen da ake tattaunawa dasu da Kidnappers din, sai a bar mutum daya wanda jami'an tsaro masu bincike za su ba shi bita.

Ina wani nazari, zanyi shawara da masana idan da hali zanyi rubutu kan tsarin da ake tattaunawa da kidnappers, yadda tsarin abin yake shine hatta kai da zaka tattauna da kidnappers da suke rike da 'dan uwanka ilmin tsaro yayi bayani akan hanyoyin tattaunawar saboda kada a samu matsala, anaso kafin ka fara magana da Kidnappers jami'an tsaro da suke yaki da kidnappers su karantar da kai tsarin

Abinda mafi yawan jama'armu ba mu fahimta a kai ba shine; fitar da irin wannan sakonni na kidnappers da yadda ake tattaunawa da su don biyan kudin fansa kara dagula al'amura suke tare da jefa rayukan wadanda suke rike a hannunsu cikin hatsari, kuma gashi bala'in sai kara yawaita yake, babu shakka ya dace a wayar da kan al'umma kan wannan matsalar

Muna rokon Allah da sunayenSa Tsarkaka ALHAYYU ALQAYYUMU Ya kubutar mana da Malam Ahmad Suleman Kano tare da abokan tafiyarsa Amin.
Daga Datti Assalafiy


No comments:

Post a Comment