Saturday, 16 March 2019

Tsoho dan shekaru 71 da ya baiwa masallata kariya aka kasheshi yayin harin masallaci a kasar New Zealand

Wannan tsohon me shekaru 71 me suna Daoud Nabi shine mutum na farko da danginshi suka tabbatar yana cikin mutane 49 da aka kashe a harin masallatan da dan ta'adda yakai a birnin ChristChurch na kasar New Zealand jiya, Juma'a.Danshi, Omar Nabi ya bayyana cewa daga kasar Afganistan suka gudo saboda tashin hankali, kuma mahaifin nasu yace yafi son zama a kasar New Zealand saboda kasace me kwanciyar hankali da dadin zama, ashe acan zai gamu da aika-aikar ta'addanci.

Omar ya bayyanawa kafar watsa labarai ta NBC cewa, a yayin da maharin ke harbin kan me uwa da wabi akan masu ibada a masallacin juma'ar, mahaifin nashi ya yiwa wasu masallata garkuwa inda maimakon a harbesu sai shi aka harbeshi da harsasai masu yawa.
Wasu rahotanni da ba'a tabbatar da su ba kuma na cewa, Daoud Nabi ne mutum na farko da maharin ya fara iskewa a bakin masallacin har ya mai maraba da zuwa dalilin haka yasa ya zama mutum na farko da maharin ya fara kashewa a masallacin.

Daoud dai na daya daga cikin wanda mutuwarshi ta fi daukar hankali a wannan harin, muna fatan Allah ya gafarta musu gaba daya yasa iya wahalar kenan.

Hakanan shima wannan bawan Allah me suna Abdi Ibrahim, ya bayyana cewa, suna tare da wannan kanin nashi Muca Ibrahim dan shekaru 3 da mahaifinsu a lokacin da maharin ya shigo masallacin, yace ya samu tsira kuma ya falfala da gudu zuwa asibiti dan ko zai ga kanin nashi amma bai ganshi ba.

Ya saka hoton kanin nashi a shafinshi na Facebook inda ya rubuta cewa daga Allah muke kuma gareshi zamu koma, zan yi kewarka dan uwana.

Akwai 'yan kasashen India, Saudiyya, Pakistan, Somalia dadai sauransu da harin ya rutsa dasu.

Yanzu haka dai an gurfanar da maharin a gaban kotu dan yankemai hukunci.

No comments:

Post a Comment