Sunday, 31 March 2019

Tsohuwa 'yar shekaru 61 ta haifawa danta, dan luwadi 'Ya

Wata tsohuwar 'yar shekaru 61 a jihar Nebraska dake kasar Amurka me suna, Cecile Eledge ta haifawa danta, Matthew Eledge, wanda dan luwadi ne da mijinshi, Elliot Dougherty diya wadda ta zama jika a gareta kenan.'Yan Luwadin biyu wanda ma'auratane sun yanke shawarar haihuwa, sai kakar daya daga cikinsu, Matthew tace zata bayar da mahaifarta dan haifa musu jaririyar da suke son haihuwa, sai Matthew ya bayar da maniyyinshi, yayin da ita kuma 'yar uwar mijin Matthew din ta bayar da kwayayenta aka hada aka sakawa tsohuwa, Cecile a mahaifarta kuma ta haifi jaririyar a Asibitin jami'ar jihar Nebraska.

Kamin yadda a sakawa tsohuwa, Cecile kwayoyin halittar haihuwar, saida aka mata gwaje-gwaje, ganin cewa ta manyan dan tantance ko zata iya haihuwar, kamar yanda Foxnews ta ruwaito.

An sakawa jaririyar da aka haifa a ranar litinin din data gabata, 25 ga watan Maris suna Uma Louise Dougherty-Eledge, yayinda mahaifan nata ke cikin farin ciki.

No comments:

Post a Comment