Monday, 11 March 2019

Tun daren jiya har yanzu mataimakin gwamnan jihar Kano na tsare a hannun 'yansanda

Har yanzu mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, yana hannun 'yan sanda, kamar yadda kakakin rundunar a jihar ya tabbatarwa BBC.


'Yan sanda sun kama Gawuna mataimakin gwamnan Kano da kuma kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo.

Rahotanni sun ce 'yan sanda sun kama manyan jami'an gwamnatin jihar ne bayan da suka yi kokarin tayar da rikici a Nasarawa, karamar hukumar da ta rage a kammala tattara sakamakon zaben gwamna a Kano.


No comments:

Post a Comment