Tuesday, 12 March 2019

Tun kamin a bayyana wanda ya lashe zaben: APC Ta Yi Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamna a Adamawa


Yayin da ake ci gaba da bayyana wadanda suka lashe zaben gwamnoni a Najeriya, kawo yanzu jam'iyyar PDP ce kan gaba a jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya inda aka bayyana sakamakon kananan hukumomi 20 cikin 21.


A sakamakon da aka fitar na kananan hukumomin 20, babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ce ke kan gaba inda ta ba jam'iyyar APC da ke mulki tazara da sama da kuri'u dubu 30.
Sai dai tuni jam'iyyar APC ta yi fatali da sakamakon zaben da ke bai wa dan takarar jam'iyyar PDP Ahmadu Umaru Fintiri zama a matsayi na gaba.
VOAhausa.

No comments:

Post a Comment