Sunday, 31 March 2019

Wadda aka zarga da amsar kudi dan wa gwamnan Kano yakin neman zabe ta mayar da martani: Lamarin ya zamar mata gobarar Titi


Bayan cece-kuce tsakanin wasu ma'abota shafin Twitter ya jawo har daya daga cikinsu ya zargi cewa an biya matasa kudi dan suwa gwamnan Kano yakin neman zabe a shafukansu , daya daga cikin wadda aka zarga da wannan lamari ta mayar da martani inda tace duk me shedar cewa an bata kudi ya fito ya fada ita kuma ta yi alkawarin bashi tukwicin Naira dubu 100.

Bayan hakanne kuma sai ta bukaci duk wanda ya saka hoto da taken Zerotension zata yi likin dinshi, hakan yasa da dama, musamman magoya bayan gwamnan Kano su kaita saka hotunansu suna cin abinci da taken na Zerotension tare da yin ba'ar cewa kudin da aka basu suwa gwamna Ganduje yakin neman zabe ne suka yi amfani dasu wajan siyan abincin.

Wannan dalili yasa taken na #zerotension ya zama na daya da aka fi tattaunawa akanshi a shafin na Twitter.

Ita kanta ta kara samun karbuwa a shafin na Twitter inda ta samu karin mabiya.

Hadimin gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasaine ne ya fara amfani da wannan take a yayin da ake tsaka da zaben gwamna a Kano kuma ubangidanshi, gwamna Ganduje ke fuskantar barazanar rasa kujerarshi, ya saka wani hoto inda yake zaune yana shan rake, ya kuma mai taken zerotention.

Gadai kadan daga cikin yanda ta kasance:

No comments:

Post a Comment