Wednesday, 20 March 2019

Wani Babban Dan Siyasa Ne Ya Turo Mu Don Mu Halaka Ahmad Sulaiman>>Masu Garkuwa Da Alaramman

Wasu Daga Kalmomin 'Yan Ta'addan Ta Wayar Salula:

"Babu matsala idan  babu kudi, mu ba saboda kudinsa muka rike shi ba, mu kudi aka bamu mu kashe shi, don wanda ya bamu aikin ya ce shi dan ta'adda ne.


"Abunda ya sa har muka yi labarin kudi, bayan mun kama shi, mun fuskanci yadda aka bamu report dinshi ba haka bane.

"Wannan abu daga sama ne, harkar siyasa ce, ba zan boye ko munafunci ba, daga Birnin Kebbi muka biyo shi.

"Abunda aka ce mana dan ta'adda ne mu kashe shi, ko da muka kama shi, muka duba gemun shi, muka ga wannan bai yi kama da dan ta'adda ba.

"Sai muka tambayeshi duk ya fada mana komai yadda al'amura suke, sai muka ga bai cancanta mu taka wata doka akan ayyukanmu ba, duk aikin da kake yi, a kanshi zaka samu duniya da lahira.

"Abunda wancan ya bamu ('Dan Siyasa ne Babba), yadda ya bamu report muka ga ba haka bane, kuma muna ji yana wa'azozi kala-kala, mu bamu san shi bane, amma ya ce mu kashe shi don abun duniya.

"Abu daya da zamu yi, ba mu ci mishi kudi ba mu yi mishi aiki ba, don haka ya maida masa kudinsa sannan ya bamu na mai, ba wani abu sai mu barshi.

"Wancan bai yiyuwa mu ci mishi dukiyarshi bamu yi mishi aiki ba, kuma ya ji mun kama shi ba wai ba mu kama shi ba.

"'Yan Siyasarku akwai 'yan matsaloli, akwai munafukai daga ciki.

"Abunda ya bamu miliyan dari uku (300) don mu kashe shi, ya ce dan ta'adda ne, sannan idan muka kashe shi fiye da wannan ma zai kara mana.

"Tun lokacin da muka zo da shi ba mu taba jikinsa, muna duba yanayin jikinsa, mun san ba yaro bane.

"Mu har an sallame mu, kuma mu ba mu ce dole sai an bamu ba.

"Sanadiyar zamansa Dattijo Masani Al-Kur'ani, idan ya biya za mu kyale shi.

"Kuma mu wannan dan siyasar ya yi mana karya, muma mun san hanyar da zamu bi ya bari, saboda bai gaya mana gaskiya ba.

"Bayan wannan babu abunda zamu yi"

Allah ya kubutar da Alaramma tare da sauran 'yan'uwa.
Rariya.


No comments:

Post a Comment