Sunday, 10 March 2019

Wata mata ta saci kuri'un zabe a Nasarawa

Masu iya magana na cewa wai rashin kunya ya amaryar kaka, irin haka ce ta faru a jihar Nasarawa, yayin da ake tsammanin maza ne ke da karfin halin kwatanta satar akwatin zabe, sai gashi an samu mace da satar kuri'u.


Matar da ta warci kuri'un a hannun jami'an hukumar zabe a mazabar Gayam, ta dankara da gudu, 'yan sanda sun bita amma suka kasa kamata, sai sojojine suka bita da gudu suka samu kwato wasu daga cikin kuri'un data warta Akan titin Makurdi, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Wani me saka ido akan harkar zaben, Mr Peter Bitrus Ya bayyanawa jaridar cewa, matar ta yi satar kuri'unne jim kadan bayan da matar gwamnan jihar, Salamatu Tanko Almakura ta kada kuri'arta a mazabar, ya ce abubuwa na tafiya lafiya lau kamin zuwan matar wadda tazo sanye da bakar doguwar riga wadda ta boye kuri'un data sata a ciki, yace wasu 'yan jagaliyar siyasa da kamar suna tare da matarne suka taimaka mata ta tsere.


No comments:

Post a Comment