Wednesday, 20 March 2019

'Yan bindigar Zamfara sunfi jami'an tsaro makamai>>Gwamna Yari

Gwamnan jihar Zamfara me barin gado, Abdulaziz Yari ya bayyana cewa, 'yan bindigar jihar sun fi jami'an tsaron dake jihar makamai, ya bayyana hakane bayan ganawar da yayi da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya bayyana cewa a wani gurin ajiye makan 'yan bindigar da aka bankado an gano bundigogin AK47 guda 500.

Gwamnan ya kuma kara da cewa, babu maganar yin sulhu da 'yan ta'addar domin sun yi yunkurin hakan a baya amma ba'a samu nasara ba.

No comments:

Post a Comment