Saturday, 9 March 2019

'Yan takara sama da dubu 1 ke fafatawa a zaben Gwamnoni

Yau Asabar ‘yan Najeriya na kada kuri’a a zaben Gwamnoni da na ‘yan majalisunsu a jihohin kasar 29, makwanni 2 bayan zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabarairu.A mukaman Gwamna 29 da za’a fafata, hukumar zaben Najeriya ta ce akwai jimillar ‘yan takara 1, da 68, yayinda a matakin ‘yan majalisun jihohi guda 991 ake da jimillar ‘yan takara dubu 14 da 583 da za su fafata a jihohi 36.

Kujerun Gwamnonin Jihohi na da matukar tasiri a siyasar Najeriya, ganin karfin fada da suke da shi a Jihohin su da kananan hukumomi da ma Tarayya.

Jam’iyyar APC yanzu haka na da kujerun Gwamnoni 22 daga Jihohi 36, yayin da PDP ke da 13, sai kuma APGA mai kujera guda.

A babban birnin tarayya wato Abuja alkalumman hukumar zaben Najeriyar ya nuna cewa za’a yi zabe a kananan hukumomi 6, wanda jimillar ‘yan 105 za su fafata, Sai kuma mukaman Kansiloli 62 da ‘yan takara 701 za su gwada sa’arsu wajen dafewa.

Baya ga zaben Gwamnonin da na ‘yan majalisunsu na jiha, akwai gundumomin da ba a kammala zaben ‘yan majalisun tarayya da aka yi tare da na shugaban kasa ba makwanni biyu da suka gabata, suma a wannan Asabar za’a kammala zabukansu a jihohi 14, da suka hada da mazabun ‘yan majalisar dattijai 7 da kuma mazabun ‘yan majalisar wakilai 24.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment