Saturday, 16 March 2019

Yanda aka min ta yi akan in karyata bidiyon Dala: Duk malamin dake cewa a zabi APC a Kano biyanshi aka yi>>Sheikh Abduljabbar

Malamin addinin Islama a Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana cewa duk malamin dake kira da a zabi jam'iyyar APC a Kano to kudi aka bashi sannan yayi kira ga malaman dasu ji tsoron Allah su daina siyasantar da addini.A wani bidiyon malamin da bayyana a shafukan sada zumunta an jishi yana cewa jam'iyyun PDP da APC duk sun mishi tayin ya musu talla amma yaki amincewa, yace musamman wakilan jam'iyyar APC suka sameshi har gida aka mai tayin miliyan 30 amma yaki amincewa.

Malamin yace an kuma mai tayin cewa yayi magana akan bidiyon dala yace karyane saboda mutane na sauraronshi amma da ya bukaci a kawomai yaga abinda masu bukatar yayi maganar suka yadda dashi sai basu sake dawowa ba.

A karshe yayi kira ga shugaban kasa,Muhammadu Buhari da ya saka baki a baiwa jama'a zabinsu a Kano, yace Obasanjo ma yayi rashin nasara ya hakura ballantana Muhammadu.

No comments:

Post a Comment