Thursday, 21 March 2019

Yayin da Abba ke shirin kai ziyara Gama, Gwamna Ganduje ya mika takardar yin taro tsawon kwanaki uku a Gama ga 'yansanda

Wasu 'yan kwankwasiyya a jihar Kano sun yi zargin cewa gwamna me ci, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kaiwa kwamishinan 'yansandan jihar takardar kama Gama har na tsawon kwanaki 3, hakan na faruwane yayin da ya rage kwanaki kadan a yi zaben raba gardama a mazabar ta Gama kuma babban abokin hamayyar gwamnan, Abba K.Yusuf ke shirye-shiryen kai ziyara Gama.Saidai me baiwa gwamnan shawara akan harkokin kakafen sada zumunta, Salihu Tanko Yakasai ya kare wannan mataki inda yace haka Kwankwaso ya yi a Bebeji inda irin wannan takardar tasa kwamishinan  yansanda ya hada dan majalisa Abdulmumin Jibril yin gangamin zabe saboda an rigashi neman izini..

Dan haka suma a wannan karin su zo da takardarsu.

No comments:

Post a Comment