Tuesday, 12 March 2019

Za mu fitar da Atletico Madrid>>Ronaldo

Dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo na fatan za su fitar da Athletico Madrid idan sun hadu a wasa na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai a ranar Talata.


Athletico ce ta ci 2-0 a wasan farko a Spaniya, inda Jose Gimenez da kuma Diego Godin ne suka ci mata kwallaye a fafatawar da suka yi a cikin watan Fabrairu.

Ronaldo baya fatan Athletico ta yi waje da su a gasar bana, domin yana son lashe kofin Zakarun Turai a Italiya kamar yadda ya yi karo da dama a Real Madrid.


Dan wasan na tawagar kwallon kafar Portugal ya ci kwallo 697 a wasa 984 da ya yi a Manchester United da Real Madrid.

Ronaldo ya ci Atletico kwallo 22 a wasa 31 a Real Madrid har da wadda ya ci a bugun fenariti a 2016, ya ce har yanzu karawar da saura za kuma su yi iya kokarinsu domin kai wa zagayen gaba.

Juventus ba a doke ta ba a gasar Serie A ta bana a wasa 27 da aka buga a wasannin, kuma doke ta da Madrid ya sa wasu na hangen za ta bi sahun Madrid da PSG wadan da aka fitar a gasar bana.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment