Friday, 29 March 2019

Zaben Gwamna:PDP tawa APC kwacen jihohi 4

Ya zuwa yanzu dai jam'iyyar hamayya ta PDP ta yiwa jam'iyya me mulki ta APC kwacen jihohi 4 a zabukan gwamna da suka wakana a fadin kasarnan.Jihohin da PDP tawa APC kwace sune:
Imo
Oyo
Bauchi
Adamawa

A jihar Imo, masu sharhi a harkar siyasa na tunanin cewa gwamnan jihar, Rochas Okorocha ne yawa jam'iyyar tashi ta APC angulu da kan zabo shi yasa bata ci zabe ba sannan kuma kasancewar ta yankin inyamurai ba abin mamaki bane dan kuwa mafi yawan jihohin yankin na PDP ne.

A jihar Oyo ma ana ganin gwamna Abiola Ajimobi Angulu da kan zabo yawa jam'iyyarshi ganin cewa bai kai labari a zaben sanata da ya nema ba haka kuma ba za'a kawar da yiyuwar rashin amsuwa da nagartar dan takarar da APC din ta tsayar ba idan aka kwatantashi dana PDP ba.

A jihar Bauchi duk da jihace ta APC, ana ganin akwai korafe-korafe da yawa da ake akan gwamna me ci, M. A Abubakar sannan fadanshi da kakin majalisar dattijai, Yakubu Dogara shima ya taimaka wajan faduwar tashi, idan ba'a mantaba a yayin da ake shirin yin zaben raba gardama a jihar har fadar shugaban kasa gwamnan yaje amma shugaba Buhari yaki ganawa dashi.

Jihar Adamawa kuwa, ana ganin akwai karfakarfar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da ta yi tasiri wajan faduwar gwamna me ci, Jibrilla Bindow, lura da rahotannin dake cewa, Atikun yayi alkawarin sai PDP ta yi nasara a jihar sannan kuma PDP ce ta yi nasara a zaben shugaban kasa a jihar, hakanan kuma akwai rahotannin dake cewa wasu manyan mutane a jihar, irin su matar shugaban kasa, A'isha Buhari da tsohon sakataren gwamnati Babachir Lawal dadai sauransu basu tare da gwamnan meci, wannan duk sun taimaka wajan faduwar APC a jihar.

No comments:

Post a Comment