Tuesday, 12 March 2019

Zabukan Pilato, Adamawa, Sokoto, Bauchi, Kano Ba Su Kammalu Ba>>INEC


Rassan hukumar zaben Najeriya ta INEC a jihohin Pilato, Adamawa, Sokoto da Bauchi da Kano, sun bayyana cewa zabukan wadannan jihohi ba su kammalu ba.
A jihar Pilato, jami’in da ke tattara kuri’u a jihar, Farfesa Richard Anande, ya ce ya ayyana zaben ne a matsayin wanda bai kammalu ba, saboda yawan kuri’un da aka soke sun fi na ratar da aka samu tsakanin jam’iyya mai mulki ta APC da abokiyar hamayyarta ta PDP.
APC ta ba PDP ratar kuri’u 44,929, wadanda ba su kai yawan kuri’un da aka soke ba, wadanda yawansu ya kai 49,377.


A jihar Adamawa haka lamarin yake, inda adadin yawan kuri’un da jam’iyyar PDP ta bai wa APC na 32,476 ya haura adadin wadanda aka soke, wato kuri’u 40,988.
A can jihar Sokoto ma, hukumar zabe ta INEC reshen jihar, ya ayyana zaben jihar a matsayin wanda bai kammalu ba, domin adadin kuri’un da suka samar da rata, wato 3,413, tsakanin PDP da APC ya gaza kuri’u 75,000 da aka soke
A Bauchi ma, jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Muhammed Kyari, ya ba da umurnin soke zaben karamar hukumar Tafawa Balewa saboda adadin ratar ya sabawa kuri’un da aka soke.
Idan aski ya zo gaban goshi, aka ce, ya fi zafi. Yanzu haka 'yan takarar gwamnan jahar Kano a karkashin jam'iyyun APC da PDP na nan sun zaku su ji sakamakon zaben gwamnan jahar Kano, daya daga cikin jahohi biyu mafiya yawa a Najeriya. Hasali ma, 'yan Najeriya da dama na dokin jin wannan sakamakon.

Jahar Kano, ta shiga cikin jerin jahohi wajen shida da hukumar zaben Najeriya (INEC) ta ayyana zabukansu a matsayin wadanda ba su kammala saboda yawan soke kuri’u. Ga dukkan alamu wadanda su ka zaku su ji sakamakon zaben jahar Kano su na da sauran jira. Da ya ke ayyana zaben na jahar Kano a matsayin mara kammala, Shugaban Hukumar Zabe ta INEC, shiyyar jahar Kano, Furfesa Bello Shehu ya ce ya zuwa lokacin jam’iyyar PDP ta ci kuri’u miliyan daya da dubu 14 da 474 a yayin da ita kuma jam’iyyar APC mai mulkin jahar ta samu dubu dari 987 da 819, a wannan zaben da kuri’u dubu 49 761 su ka lalace.
Furfesa Shehu ya ce an soke jimlar kuri’u dubu 141 da 694 a runfunan zabe wajen 172 a fadin Kano. Ya ce PDP ta zarce APC da kuri’u dubu 26 da 655, to amma dayake kuri’un da aka soke dubu 141 da 691 ne, tanajin hukumar zabe ya hana ayyana irin wannan zaben a matsayin kammalalle. Dalili kuwa shi ne hakan ya hana tabbatar da tazarar da ake bukata tsakanin ‘yan takarar biyu kafin a tabbatar da sakamakon zaben, ma’ana a tabbatar da kammalar zabe. Don haka hukumar zaben ta ayyana zaben na Kano a matsayin mara kammala, kuma za a sanar da ranar da za a sake gudanar da zaben a wuraren da aka soke.
VOAHausa

No comments:

Post a Comment