Wednesday, 13 March 2019

Zakarun Turai: Man City ta yi waje da Schalke 7-0

Manchester City ta caskara Schalke 7-0 a karawa ta biyu ta Zakarun Turai ta tabbatar da wucewarta matakin dab da na kusa da karshe.


Sergio Aguero ne ya fara daga raga da bugun fanareti, sannan ya kara ta biyu bayan minti uku, bayan da Raheem Sterling ya sa masa wata bal da dunduniya.

Leroy Sane ya jefa ta uku sannan kuma ya bayar da bal har sau uku aka ci bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, lokacin da Man City ta shiga daga raga ba ji ba gani.

Sterling da Bernardo Silva da Phil Foden da kuma Gabriel Jesus dukkaninsu kowa ya ci, wanda a karshe City ta yi nasara da ci 10-2, jumulla gida da waje.

An fitar da Manchester City wadda ta farfado daga baya a karawarsu ta farko a Jamus ta yi nasara da ci 3-2, a wasan dab da na kusa da karshe a shekarar da ta wuce a haduwarsu da Liverpool, kuma ba ta taba cin kofin na Zakarun Turai ba.

A ranar Juma'a ne za a fitar da jadawalin wasan matakin na dab da na kusa da karshe, na kungiyoyi takwas da karfe 11 na safe agogon GMT.

Kasancewar Bayern Munich ko Liverpool daya za ta yi waje daga gasar a daren Larabar nan, kuma Juventus ta yi waje da Atletico Madrid, Guardiola zai kara samun kwarin gwiwa na cin kofinsa na Turai karo na uku.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment