Tuesday, 12 March 2019

Zan baiwa PDP mamaki>>Gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ko kadan be kaduba da abinda ke faruwa a jiharshi ta Kano ba kuma PDP ta shirya shan mamaki dan kuwa guraren da za'a sake zabuka duk magoya bayanshine.A sanarwar da kwamishina  watsa labarai, matasa da Al'adu wanda kuma shine jami'in watsa labaran gwamnan a kan harkar zabe, Malam Muhammad Garba ya fitar yace duk da magudin da PDP ta yi a zaben ta hanyar sayen kuri'u, APC ko gezau ba ta yi ba dan tana da tabbacin cewa zabukan da za'a sake itace zata lashe su, kamar yanda The Nation ta bayyana.

Yace a yanzu sun sake shiri dan kuwa sun toshe duk wata kafa ta magudin zabe da sayen kuri'u da ka iya faruwa a zaben da za'a sake kuma sun san APC ce zata yi nasara.

No comments:

Post a Comment