Wednesday, 20 March 2019

Zanga-zanga Ta Biyo Bayan Umarnin Kotu Na Dakatar Da Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Bauci


Zanga-zangar tir da matakin tsaida ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan Bauchi ne ke ci gaba da daukan sabon salo, inda masu zanga-zangar suke ta cewa basu yarda da neman take masu hakki ba.


Masu zanga-zangar dai sun mamaye daidai shingen da jami’an tsaro suka sanya a hanyoyin shiga ofishin INEC da ke Bauchi suna masu rera wakoki daban-daban da ke cewa su Kaura suke so ba M.A ba.
Mata da matasa ne dai suka fi yawa a cikin masu shiga Zanga-Zangar, a gefe guda kuma jami’an tsaro sun kara karfi sosai domin baiwa INEC din kariya.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment