Saturday, 16 March 2019

Zidane ya fara wasa da kafar dama: Madrid 2-0 Celta Vigo

A wasanshi na farko tun bayan dawowa da aikin horas da 'yan wasan Real Madrid, Zinedine Zidane ya fara da kafar dama inda Madrid din ta lallasa Celta Vigo da ci 2-0, saidai abu da ya fi daukar hankula a wasan shine itin canje-canjen 'yan wasan da aka samu.Zidane bai fara wasa da gola, Thibaut Courtois ba inda ya canjashi da Keylor Navas haka kuma ya saka 'yan wasa, Isco da Marcelo wanda duk a zamanin tsohon me horaswa, Santiago Solari be cika yi dasu ba.

Isco ne ya fara cin kwallo sannan daga baya Bale ya saka ta biyu a nasarar Madrid din ta farko cikin wasanni tara da ta buga.

Wannan dai za'a iyq cewa nasara ce me kyau, saidai abin jira a gani shin zata dore ko kuwa?

Lokaci ne dai zai bayyana haka ga me tsawon rai.

No comments:

Post a Comment