Monday, 1 April 2019

A karin farko tun bayan lashe zabe: Shugaba Buhari zai yi tafiya zuwa kasar Senegal

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai tafi Dakar, Baban birnin kasar Senegal a yau, Litinin inda zai halarci taron kaddamarwa na shugaban kasar, Macky Sall bayan lashe zaben da yayi a karo na biyu.Shugaba Sall ne ya gayyaci shugaba Buhari halartar taron, kasancewashi shugaban ECOWAS, shugaba Buhari zai zama babban bako a gurin taron da manyan shuwagabannin kasashen Afrika zasu halarta da zai wakana gobe, Talata.

Shugaban zai samu rakiyar gwamnonin Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, dana Bauchi, Muhammad Abubakar, dana Nasarawa, Tanko Almakura.

Sauran wanda zasu wa shugaban rakiya sune ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, da me baiwa shugaban shawara akan harkar tsaro, Majo Janar Babagana Mongun, dadai sauransu, kamar yanda yake kunshe a cikin sanarwar da me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar.

No comments:

Post a Comment