Tuesday, 16 April 2019

A karin farko za'a saka sa hannun mace akan takardar kudin Najeriya

A karin farko a tarihin Najeriya za'a saka sa hannun mace a kan takardar kudin Nara. Wadda za'a saka sa hannun nata itace, Priscilla Ekwere Eleje wadda a baya itace daractar kudi ta bankin ta riko amma a yanzu an tabbatar da ita a matsayin daraktar dindindin.Tabbatar mata da wannan matsayi yasa yanzu sa hannunta zai kasance akan takardun kudin Naira na Najeriya.

Ladi Kwali, wadda ta kasance me hada abubuwan laka itace kadai mace data kasance akan takardar kudin Naira wadda a kowace Naira Ashirin ana ganin hotonta.

Kamin wannan lokaci dai dukkan kudin Naira na dauke ne da hotuna da kuma sa hannun maza.

No comments:

Post a Comment