Sunday, 14 April 2019

Abba K. Yusuf ya roki wata yarinya masoyiyarshi data tsaya da azumin da take yi sabodashi

Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar PDP, Abba K. Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida kenan a wadannan hotunan tare da wata yarinya da ta dauki azumi tun ranar 9 ga watan Maris da aka dage zaben jihar sannan taki ajiye azumin da zummar sai ranar da kotun saurarren karar zabe ta bashi nasara.Abban ya hadu da yarinyar da mahaifiyarta inda ya roketa da ta ajiye azumin da take yi sannan ya bata tabbacin cewa a bayyane abin yake cewa shine yaci zaben kuma nan bada dadewa ba kotu zata tabbatar dashi a matsayin gwamnan jihar Kanon.

No comments:

Post a Comment