Friday, 12 April 2019

Abba Yusuf na kalubalantar nasarar Ganduje a kotu


media
Jam’iyar PDP reshen jihar Kano ta shigar da karar APC a gaban kotu, in da take kalubalantar nasarar da Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaben da aka gudanar. Kwanaki 20 kenan da Hukumar Zaben Najeriya Mai Zaman Kanta, INEC ta ayyana Ganduje a matsayin wanda ya yi nasara.

Takardar korafin da PDP ta rubuta wa kotun sauraren korafe-korafen zabe, na cewa, dan takaranta Abba Yuusf ne ya samu nasara a zaben da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris da ya gabata.
Kazalila jam’iyyar adawar na korafin cewa, Hukumar INEC ba ta gudanar da zaben cikin mutunta dokoki da kundin tsarin mulkin kasar ba.
A yayin zantawa da manema labarai, Abba Yususf ya ce, PDP ta samu mafi yawan kuri’u a kananan hukumomi 44 a zaben na ranar 9 ga watan Maris.
A cewar Yusuf, suna addu’ar  kotun za ta fayyace hakikanin wanda ya yi nasara a zaben.
Jam’iyyar ta PDP ta bayyana cewa, matakin ayyana zaben ranar 9 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba, wani yunkuri ne na samar wa APC hanyar magudin dawo da dan takaranta akan karagar mulki.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment