Friday, 12 April 2019

Abinda Messi ya gayamin bayan dana fasa mai hanci>>Smalling

Tauraron dan kwallon kafar Manchester United, Chris Smalling ya bayyana abinda Lionel Messi na Barcelona ya gayamai bayan karon battar da suka yi a lokacin wasan cin kofin Champions League da suka buga da yayi sanadiyyar fashewar hancin Messin.


Da yake magana da BBC Radio, Smalling ya bayyana cewa, bayan kammala wasan sun yi magana shi da Messi kuma Messing ya gayamai cewa abinda ya faru tsakaninsu tsautsai ne, sun gaisa sannan kuma sun wa juna fatan Alheri.

Hakanan Smalling ya kara da cewa, bayan wasan sun kuma yi magana da Suarez wanda shima sun sha gumurzu a filin wasan inda ya gaisa shima sukawa juna fatan Alheri.

Yace abune me kyau irin yanda ake fafutuka a fili sannan idan sun gama kuma a rika girmama juna.

No comments:

Post a Comment