Sunday, 14 April 2019

Adadin Kuri’un Da Atiku Ya Yi Ikirarin Samu Ba Gaskiya Ba Ne>> INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta nesanta kan ta daga adana wani sakamakon zabe wanda dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar y ace ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 Ga Fabrairu.


INEC ta fadi haka ne a cikin wani martani da hukumar ta yi kan ikirarin da Atiku ya yi a cikin karar da ya gabatar ga Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa, inda ya kalubanci sakamakon zaben.

Lauyan INEC, Yunus Usman (SAN), ya bayyana cewa ko kusa ba a tattara sakamakon zaben shugaban kasa ko watsa shi a na’urorin sadarwa ba.

INEC ta kara da cewa babu wani rumbun na’urar da ta tattara ko ta killace sakamakon zaben 2019 a ciki, ballantana har a ce Atiku ya shiga ya leko sakamakon zaben da ya yi ikirarin cewa shi ya samu.

Atiku ya yi ikirarin cewa kuri’u 18,356,732 ya samu, shi kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya samu 16,741,430.
Atiku ya ce ya yi nasara a kan APC da kuri’u 1,615,302. Sai dai kuma INEC ta ce wannan duk shaci-fadi ne da zuki-ta-malle, amma babu inda INEC ta killace sakamakon nzabe a na’urar zamani da har Atiku ya shiga ya dubu, ko wani ya shiga ya dubo masa.

Darakan Yada Labarai da Fasahar Zamani na INEC, Chidi Nwafor ne maimaita haka a cikin bayanin da INEC ta tura wa kotu a rubuce cewa zargin da Atiku ya yi ba gaskiya ba ne.

Ya ce Buhari ya yi nasara ne bisa zaben sa da aka yi, amma babu wani sakamako na daban, wanda Atiku ya yi ikirarin cewa sakamakon wai ya nuna shi ne ya yi nasara.

Nwafor y ace iyakar adadin kuri’un da Atiku ya samu, su ne Milyan 11,262,978. Don haka ba shi ne ya yi nasara ba, Buhari ne ya yi nasara da kuri’u milyan 15,191,847.
Rariya.


No comments:

Post a Comment