Tuesday, 2 April 2019

Ahmed Musa ya lashe kyautar dan kwallon mafi shahara ta 2018

A bikin karrama 'yan kwallon kafar Najeriya da aka gudanar a daren jiya wanda hukumar kula da kwallon kafar Najeriya, NFF a takaice da hadin gwiwar kamfanin Aiteo, Ahmed Musa ya samu kyautukan tauraron dan kwallon kafa na Najeriya ajin maza da kuma kyautar kwallo mafi shahara, kwallo ta biyu da ya ci kasar Iceland a gasar cin kofin Duniya data gabata.
Sannan kuma magoya bayan kungiyar Kano Pillars ne suka samu kyautar taurarin magoya bayan kungiyar kwallo ta Najeriya.

No comments:

Post a Comment