Tuesday, 30 April 2019

Ajax ta ci Tottenham 1-0: Muhimman abubuwan da suka faru a wasan


Kungiyar kwallon kafa ta Ajax ta bi Tottenham har gida ta cita 1-0 me ban haushi a wasan kusa da na karshe da suka buga na neman daukar kofin Champions League. Van de Beek ne ya ciwa Ajax kwallon ana cikin mintuna 15 da fara wasa.

Van De Beek ya jera wasanni biyu kenan yana cin kwallaye a wasannin da kungiyarshi taje bakunta a gasar ta Champione League, ta karshe itace wadda yaci Juventus.

Ajax ta ci wasannin da ta je bakunta sau uku a jere kenan a gasar ta Champions League, inda taci Real Madrid, Juventus, yanzu kuma ga Tottenham.

Wannan kwallon da Ajax taci ta bata damar zama mafi samun damar zuwa matakin wasan karshe a gasar, saidai a mako me zuwa Tottenham zata bi Ajax gida inda za'a buga wasan kusa dana karshen mataki na biyu. A wasan da Tottenham zata bi Ajax gida tauraron dan wasanta da aka dakatar, Heung-Min Son zai dawo, sannan Ajax bata cin wasanninta na gida, idan hakan ta kasance Tottenham zata iya yin nasara ta kai matakin wasan karshen duk da nasarar da Ajax ke da ita yanzu.

Wani abu da aka lura dashi a wannan wasan shine, Ajax ta koma tana wasan tare gida wanda ba'a saba ganinta da yin haka ba, Ajax ta saba fitowa ta nemi kwallo amma a daren yau sai salon wasanta ya canja, musamman da aka dawo hutun rabin lokaci.

Dan wasan baya na Ajax me shekaru 19, Matthijs de Ligt yayi kokari sosai a wasan kuma shine dan wasan mafi karancin shekaru da ya taba zama kaftin din kungiyar da ta buga wasan kusa dana karshe a gasar Champion League.

Rugun tsumin da aka samu tsakanin dan wasan Tottenham, Vertonghen da dan garinshi, Toby Alderweireld da golan Ajax, Andre Onana, ya bar Vertonghen din kace-kace cikin jini wanda har saida likitocin kota kwana suka dubashi aka kuma fita dashi wajen fili, saidai daga baya ya dawo amma bayan lokaci kadan aka sake fitar dashi saboda matsalar. Tottenham ta sako Sissoko a madadinshi wanda ya sanya kungiyar ta taka kwallon da kyau.


No comments:

Post a Comment