Tuesday, 16 April 2019

Ajax ta fitar da Juventus daga Champions League: Juventus ta yi asarar sayen Ronaldo: Karanta karin muhimman bayanai akan wasan na yau

Kungiyar kwallon kafa ta Ajax ta fitar da Juventus daga gasar cin kofin Champions League bayan da ta ci ta jimullar kwallaye 3-2. A wasan da suka buga a daren yau, Talata, duk da Ronaldo ya ci kwallonshi ta 126 a gasar amma Ajax sun ci kwallaye 2 wanda hakan yasa aka tashi 2-1.Rabon da Ajax ta je wasan daf dana karshe a gasar Champions League tun kakar 1996-97 kusan shekaru ashirin da biyu kenan.

Sannan a karon farko cikin shekaru 9 kenan Ronaldo be kai ga wasan kusa dana karshe ba a gasar.

Bayan kammala wasan, Anga Ronaldo cikin damuwa inda ya rufe fuskarshi sannan daga baya ya fice daga filin wasan.

Wani abin mamaki shine har magoya bayan juventus sun amince da cewa Ajax ce ta cancanci yin nasara a wasan saboda yanayin kwallon da suka buga.

Wannan nasara dai zata iya zama ramuwace Ajax din ta yi akan Juventus domin a shekarar 1996 Juventus ce ta cire Ajax a wasan karshe na gasar sannan kuma saa shekara me bi mata ma Juventus din ce dai ta sake cire Ajax din.

Hakanan masu sharhi aka al amuran wasanni sun bayyana cewa a ma'aunin tattalin arziki da kuma kashe kudi wajan cefanen 'yan wasa ko kusa Ajax bata kami kafar Juventus ba amma duk da haka hakan baiyi tasiri ba wajan wannan wasa.

Da dama sun bayyana sayan Ronaldo da Ajax ta yi a matsayin asara dan dama butinsu na kawoshi shine dan su ci kofin Champions League.

Hakanan bayan wasan an ga wasu magoya bayan Juventus na kuran da a kori me horas da kungiyar, Allegri inda sukace zamanshi baida amfani.

Wasan na yaudai yayi zafi ta yanda saida akata amfani da na'aurar taimakawa alakalin wasa a lokuta daban-daban

Hakanan fitar da Juventus daga gasar ta nuna cewa Ronaldo bazai cimma burinshi na nunawa me kungiyar Real Madrid, Florentino Perez cewa zai iya cin Champions League ko da ba a Madrid ba wasu na ganin idan Marid ta kadu ta tafiyar Ronaldo to shima barinta ya taba shi.

No comments:

Post a Comment