Tuesday, 30 April 2019

Al'aurar wata mata ta zazzago yayinda take tsaka da motsa jiki


Wata tsohuwa 'yar shekaru 60 da haihuwa ta garzaya asibiti bayan da ta yi aikin motsa jiki kuma taji kamar mahaifarta ta zazzago. Lamarin ya farune a birnin Xuzhou na kasar China kamar yanda Daily Mail ta ruwaito.

Tsohuwar wadda ba'a bayyana sunanta ba ta gayawa likita cewa tana cikin motsa jiki sai ta ji alamar kamar mahaifarta ta zazzago shine ta zo dan a dubata.

Likitan data dubata tace sun ga mahaifartace ta zazzago kuma hakan bashi da nasaba da motsa jikin da take yi, hakan yakan faru ga wasu daidaikun matan da suka haihu da yawa a baya sannan kuma suka manyanta.

No comments:

Post a Comment