Monday, 1 April 2019

Alex Iwobi ya koma Barcelona: Yanzu yafi kowane dan wasan Afrika tsada

Tauraron da kwallon Najeriya dake bugawa kungiyar Arsenal wasa, Alex Iwobi wanda a baya akaita alakantashi da komawa kungiyoyin, PSG, Real Madrid dadai sauransu yanzu ya koma Kungiyar Barcelona.Barcelona ta sayi Alex Iwobi, wanda tuni yasa hannu a yarjejeniyar buga mata wasa ta tsawon shekaru 4 akan kudui fan Miliyan 90, kamar yanda Goal ta ruwaito.

Da wannan ne Iwobi ya zama dan wasan da yafi kowane dan wasa tsada a nahiyar Afrika.

Dan shekaru 22 ya je Barcolana da yammacin jiya, Lahadi a jirginshi inda aka mai gwaje-gwajen lafiya, sannan ya saka hannu a yarjejeniyar bayan da a lokuta da dama a baya ya musanta komawa Barca.

Ya gayawa manema labarai cewa, ina farin ciki da dawowa Barcelona a wannan kakar wasa.

Ya kara da cewa, Barcelonace babbar kungiya a Duniya kuma ina sa idon fara aiki da Ernesto Valverde da Lionel Messi dan bayar da gudummuwata wajan ganin kungiyar ta kai ga nasara.

No comments:

Post a Comment