Thursday, 11 April 2019

Ali Nuhu ya maka Adam A. Zango a kotu bisa bata suna: Karanta Martanin Adamun

Fadan dake tsakanin taurarin fina-finan Hausa, Adam A. Zango da Ali Nuhu ya dauki sabon juyi inda a yanzu Alin ya maka Adamu a kotu bisa zargin bata masa suna.Adamunne ya saka sammacin da kotun USC dake Fagge Kano ta aike mai na karar da Alin ya kai akanshi inda kotun ta bukaci ya bayyana a gabanta nan da ranar 15 ga watan Aprilu, watau Litinin me zuwa.

Adam A. Zango dai a martani ga wannan sammaci yace "ALHAMDULILLAH ALLAH YASA MU DACE! ALLAH YASA MUNA DA TSAWON RAI. NA BAYAR DA RAINA FANSA AKAN MUTUNCIN UWATA DA MUTUNCINA KUMA BAZAN TABA YIN DANA SANI BA KO MENENE ZAI FARU DANI."

Adamun dai ya rama zagin da yace Alin Nuhunne kesa yaranshi na mai akan Alin amma daga baya yace an bashi baki ya kuma cire zagin yace komai ya wuce.

Yanzu dai abin jira a gani shine yanda zata kaya a kotu.

No comments:

Post a Comment