Sunday, 14 April 2019

Amina Amal Ta Kwanta Jinya Bayan Dukan Da Hadiza Gabon Ta Yi Ma Ta

Jaruma Amina Amal ta kwanta rashin lafiya bayan dukan da kawo wuka da fitacciyar Jaruma Hadiza Gabon ta yi ma ta tare da taimakon wasu karti maza.


Majiyar LEADERSHIP A YAU ta tabbatar da cewa, a yanzu haka yarinyar ta na fama da yanayi na rashin lafiya da kuma rudewa sakamakon mumman tashin hankalin da ta fuskanta tun a daren farko da Jaruma Gabon da tawagarta su ka far ma ta a gidanta da ke Kaduna.

Idan za a iya tunawa, Amal ta dora wani hotonta ne a Instagram wanda ke nuna cibiyarta a waje, lamarin da janyo zafafan martani daga masu yin sharhi a kan hoton, ciki har da wasu daga cikin ‘yan fim, kamar ita Gabon da Jaruma Aisha Tsamiya da Darakta Hassan Giggs da sauransu. To, amma abin mamaki shi ne Gabon ce kadai wacce Amal ta mayar wa da martani ta hanyar yin shagube kan dabi’a ta madigo, lamarin da ya fusata Gabon din.


Majiya mai tushe ta labarta wa wakilinmu cewa, sau uku ‘yan tawagar sun hada da maza kamar guda biyar ko shida, wadanda wasunsu a motar Hadiza Gabon din su ke yayin da wasu kuma su ke cikin babur din Adaidaita Sahu, cikinsu har da wasu fitattun ‘yan fim guda biyu; daya darakta ne ma.

Haka nan an ji Gabon din ta na waya da wani fitaccen darakta kuma jarumi, wanda ta kira da “Baba” a lokacin da su ke yin dukan na biyu, inda ta ke labarta ma sa cewa, sun kama Amal kuma ta sa a na lakada ma ta duka a lokacin.

Majiyar ta kara da cewa, sun fara yin kicibis da Amal ne a kofar gidanta bayan da su ka yaudare ta hanyar umartar wata kawarta da ta kira ta a waya ta tambaye ta inda ta ke a daren. Tun a kofar gidan su ka fara lakada yarinyar, amma yayin da mutanen da ke kusa da gidan su ka fara kawo jiki, sai su ka janye ta zuwa cikin gidan, inda a can ne su ka yi abinda su ka yi har su ka yi ma ta bidiyo.

Majiyar ta kara da cewa, a na zargin har sai da su ka danne ta su ka dura ma ta kayan maye, don ta fadi abinda su ke son ta furta a bidiyon da Gabon din ta dauke ta lokacin dukan.

A daren ne masu kai farmakin su ka tafi da wayar yarinyar. Daga nan ne fa bayan Amal ta farfado ta nemi da a dawo ma ta da wayarta, amma sai ita Gabon ta ba ta sharadin cewa, sai dai ta zo ta dauke ta a bidiyo ta na ikirarin cewa sharri ta yi ma ta, kafin ta mayar ma ta da wayar. Wannan ya kai ga a ka ga Amal a wani bidiyon ta na karyata kanta, don kawai ta amshi wayarta.

A yanzu Amal ta bar Kaduna, saboda hatsarin da rayuwarta ke ciki bisa hasashen za a iya daukar nauyin ‘yan ta’adda su sake kai ma ta hari. To, amma jim kadan bayan hakan sai ta kwanta jinya sakamakon barazanar da ta fuskanta, inda yanzu haka likitoci na kokarin ceto rayuwarta ne, saboda a na kyautata zaton cewa, lamarin ya haifar ma ta da ciwo a zuciyarta.

Za mu cigaba da kawo mu ku karin bayanai in sha Allahu.
Leadershipayau.

No comments:

Post a Comment