Tuesday, 16 April 2019

Amina Amal ta maka Hadiza Gabon a kotu: Ta bukaci ta biyata miliyan 50 a matsayin diyyar cin zarafin data mata

Jarumar fina-finan Hausa, Amina Amal ta maka abokiyar aikinta, Hadiza Gabon a kotu bisa zargin cin mata zarafi dan haka ta bukaci kotu da ta sa Hadizar ta biyata diyyar miliyan 50 da kuma wallafa bata hakurin cin zarafin data mata a manyan jaridu guda biyu na kasarnan.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito sammacin da kotu ta aikewa Hadizar na kararta da Amina Amal din takai babbar kotun gwamnatin tarayya dake Kano.

Amal dai ta saka wasu hotuna da suka jawo cece-kuce a shafinta na Instagram wanda bayan masoyanta hadda wasu daga cikin manyan jarumai abokan aikinta sun yi Allah wadai da hotunan ciki kuwa hadda Hadiza Gabon din.

Wannan yasa Amal din ta mayar da martani da wani sako a shafinta inda tawa wata jaruma gargadin cewa zata tona mata asiri idan bata daina shiga harkar ta ba, bayan nan ne sai wasu hotunan bidiyo suka bayyana inda aka ga Amal din na bayar da Hakuri ga Hadizar.

Ga takardun sammacin kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.No comments:

Post a Comment