Friday, 12 April 2019

An dakatar da Diego Costa buga wasa 8

An dakatar da Diego Costa buga wasa takwas, an kuma ci shi tara kan samun sa da laifin cin zarafin alkalin wasa.


An bai wa dan kwallon jan kati a wasan hamayya a gasar La Liga da Barcelona ta yi nasara da ci 2-0 a Camp Nou ranar Asabar.

A rahoton da alkalin wasa Jesus Gil Manzano ya rubuta, bayan da aka tashi daga karawar ya ce Diego Costa ya ci mutuncin babarsa - zargin da dan kwallon Spain ya musanta.

Hukumar kwallon kafar Spaniya ta ce ta dakatar da dan kwallon wasa hudu sabo da zagin babar alkali da ya yi da kuma wasu hudu sakamakon rike alkalin gam da ya yi.

Hakan na nufin Costa ba zai buga wa Atletico saura wasa bakwai da suka rage a gasar La Liga ba, da kuma guda daya a kakar badi ba.

Haka kuma Costa zai biya tara har da Atletico Madarid ma.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment