Sunday, 14 April 2019

An fitar da jadawalin Gasar Kasashen Afrika ta bana


media
An kammala bikin fitar da jadawalin kasashen da za su fafata da juna a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika, wadda kasar Masar za ta karbi bakwanci daga ranar 21 ga watan Juni zuwa 19 ga watan Yuli. Masar mai masaukin baki ce za ta fara kece raini da Zimbabwe a rukunin A, yayinda Najeriya ta fada a rukunin B, in da za ta kara da Guinea da Madagascar da Burundi.

JADAWALIN KASASHEN DA ZA SU FAFATA A GASAR AFRIKA A MASAR
RUKUNIN A:
Masar, Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Uganda da Zimbabwe
RUKUNIN B:
Najeriya, Guinea, Madagascar da Burundi
RUKUNIN C:
Senegal, Algeria, Kenya da Tanzania
RUKUNIN D:
Morocco, Ivory Coast, Afrika ta Kudu da Namibia
RUKUNIN E:
Tunisia, Mali, Mauritania da Angola
RUKUNIN F:
Kamaru, Ghana, Benin da Gunea-Bissau.
A karon farko kenan da kasashe 24 ke fafatawa a wannan babbar gasar ta Afrika wadda aka fara gudanar da ita shekaru 62 da suka gabata.
A shekarar 1957 aka fara gudanar da gasar a Sudan, in da a wancan lokacin kasashen Sudan da Masar da Habasha suka kece raini da juna, yayinda Masar ta lashe kofin a wancan lokacin.
Kasar Masar ce ta fi kowacce kasa daukar kofin gasar, in da ta lashe har sau bakwai, sai Kamaru da ta lashe sau biyar kuma a halin yanzu ita take rike da kambi. Najeriya ta lashe kofin sau uku, yayinda Ghana ta lashe sau hudu.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment