Tuesday, 30 April 2019

An hana mata sanya Nikabi a Sri Lanka

Sakamakon harin ta'addancin da aka kai a Sri Lanka, gwamnatin kasar ta hana mata Musulmai saka Nikabi.


Sanarwar da aka fitar daga Fadar Shugaban Kasar ta ce, an hana saka duk wani nau'in tufafi da zai rufe fuskar mutum ko wanda zai hana jami'an tsaro gudanar da aiyukansu yadda ya kamata.

An bayyana cewar a yayin zaman majalisar Ministoci a makon da ya gabata ne aka gabatar da wannan kudiri.

Daga ranar Litinin din nan an fara aiki da dokar da ta hana saka Nikabi ko tufafin da zai hana jami'an tsaro tantance mutum.

A ranar 21 ga watan Afrilu ne a yayin da Kiristoci ke bukin Ista aka kai hare-haren kunar bakin wake a wasu Majami'u da gidajen otel inda aka kashe mutane 253.

Kungiyar ta'adda ta Daesh ce ta dauki alhakin kai harin.
TRThausa.No comments:

Post a Comment