Friday, 12 April 2019

An kama Julian Assange a Landan


An kama daya daga cikin wadanda suka kafa kamfanin kwarmata bayanai na Wikileaks, Julian Assange, a ofishin jakadancin kasar Ecuador da ke birnin Landan.


Assange ya boye a cikin ofishin tun a shekarar 2012 domin gujewa tasa keyar sa zuwa kasar Sweden bisa wasu tuhume-tuhume da akayi masa.
Julian Assange
An same shi da laifin kin bayyana a gaban kotun Majistra da ke Westminster a ranar Alhamis.
A yanzu Amurka na tuhumar shi da falassa wasu manyan bayanan sirrinta.
Birtaniya za ta yanke hukunci ko za a tasa keyarsa, a matsayin martani kan zarge-zargen da ma'aikatar shari'a take masa a inda ta ce ya hada baki da tsohon mai sharhi kan leken asiri, Chelsea Manning wajen satar rumbun bayanai sirri guda hudu.
Yana fuskantar daurin shekara biyar a gidan yarin Amurka idan an same shi da laifukan hada baki wajen yin kutse a kwamfuta.
Shugaban Ecuador ya ce ya janye kariyar da ake bashi saboda zamansa dan kasar, bisa keta dokokin kasa da kasa da ya yi ta yi.
Amma Wikileaks ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Ecuador ta ki bin hanyoyin da suka kamata wajen kwace kariyar da ake bai wa 'yan kasar daga hannun Assange bayan da ya keta dokokin.
Za a kai Assange, mai shekara 47, zuwa wani ofishin 'yan sanda da ke tsakiyar birnin Landan kafin ya bayyana a gaban kotun Majistrin Westminster.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment