Monday, 15 April 2019

An kawar da cutar kurkunu a Najeriya idan kuma kasan wani me ita, ka kawoshi za'a biyaka kudi


Wani kwararre a harkar kimiyyar lafiya, Prof. Luke Edungbola ya kalubalanci duk wani dan Najeriya daga kowane bangare ya kawo mishi mutun koda dayane dake da cutar kurkunu shi kuma zai bashi kyautar kudi.


Prof. Luke Edungbola yace babu sauran cutar kwata-kwata a Najeriya.

A cikin wata wallafa da yayi daga jami'ar Ilori ya bayyana cewa ya samu damar yin aiki tukurune wajan kawar da cutar bayan da jami'ar ta Ilori ta bashi goyon baya da karfin gwiwa, ya ce mtasaloli irinsu matsalar tsaro, jahilci, rashin kyawun gurin zama da rashin tsaftataccen ruwansha musamman a yankin Arewa maso yamma sun taimaka wajan yaduwar cutar. Amma yace a karshe ya samu nasara.

Yace ya samu hadin kai da kuma gudummuwar masu ruwa da tsaki a harkar lafiya wajan gudanar da wannan aiki, sannan kamin ya dukufa kan wannan aiki na kawar da cutar ta kurkunu, Najeriya ce kan gaba a yankin Sahara wajan yawan cutar.
NAN.

No comments:

Post a Comment