Wednesday, 17 April 2019

An kawo kofin Champions League Najeriya

Kamfanin giyar Heineken wanda shine ke daukar nauyin gasar cin kofin Champions League ya kawo kofin na Champions League Najeriya tare da tsohon dan wasan Barcelona Puyol.Kamfanin ya kai kofin fadar gwamnatin jihar Uyo inda suka gayyaci gwamnan jihar, Udom Emmanuel  da ya zo kallon wasan da za'a buga a filin wasan jihar tsakanin Puyol da Okocha da wasu kwastomomin kamfanin.

Kofin zai kwashe kwanaki 3 a Najeriya inda za'a kaishi Uyo da Legas.


No comments:

Post a Comment