Thursday, 4 April 2019

An Kori Wani Sojan Da Ya Aikata Fyade Ma Yarinya A MaiduguriWata kotun soja ta musamman da ke da zama a garin Maiduguri ta yanke hukuncin kora ga wani jami’in sojan sama, da ake zargin ya yi wa wata yarinya yar sheakru 14 fyade.


Wannan kotun soja ta musamman da ke karkashin, Manjo-Janaral Yakubu Auta, ta yanke hukuncin korar sojan saman, Flight Lt. Matins Enweran, wanda dan asalin jihar Imo, saboda da yin lalata da Zahra Ali yar gudun hijira da ta fito daga garin Marte tare da iyayenta da su ke samun mafaka a garin Maiduguri.
Zahra ta na zaune tare da iyayenta a wani sansanin yan gudun hijira mai suna Bakasi, ta fita tare da kawayenta zuwa bayan gari domin neman itacan da za su hura wuta, wanda adaidai wannan lokacin ne su ka yi arangama da sojan da ya dauke ta zuwa cikin dajin da ya aikata lalata da ita.
VOAhausa.

No comments:

Post a Comment