Tuesday, 30 April 2019

An saki Zainab Aliyu a Saudiyya

Hukumomin Saudiyya sun saki Zainab Aliyu a birnin Jeddah ranar Talata.

Babban sakatare a ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya Mustapha Suleiman ya tabbatarwa BBC wannan labarin.


Ya ce "an rubuta wa jami'an gwamnatin Saudiyya takardu kamar yadda aka tsara a harkokin diflomasiyya, an ta bayanai."

"Kuma an nuna musu gaskiya wadannan mutane da kuma irin kokarin da gwamnati ta yi daga gida wajen kama su wadanda ake zargin cewa su ne suka sanya musu kwayoyi a jakunkuna," in ji shi.


Ya ci gaba da cewa "saboda haka wannan al'amari da Allah Ya warware ta hannun wadanda jami'ai da hukumomi kasashen biyu.

Daga nan ya yi godiya ga hukumomin Saudiyya dangane da hadin kan da suka ba mu a kan "wannan al'amari mai wuyar wararewa."

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan kafafan sada zumunta Bashir Ahmed ya bayyanaa wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment