Saturday, 13 April 2019

An Sasanta Ali Nuhu Da Adam A. Zango A Kano

Hadaddiyar kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta kasa, MOPPAN, karkashin jagorancin Malam Abdullahi Maikano, ce ta yi wannan aiki a ofishin dattijon Kannywood kuma shugaban majalisar amintattu na kungiyar, wato Malam Abdulkarim Mohammed a yau Asabar.


Sakataren kungiyar MOPPAN reshen jihar Kano, Malam Salisu Officer, shi ne ya tabbatar da wannan bayani, yana mai cewa, yanzu Ali zai janye karar da ya kai Adamu.


No comments:

Post a Comment