Thursday, 11 April 2019

An wallafa hoton 'Black Hole' na farko

Masanan sararin samaniya sun dauki hoto na farko na wani katon rami a sararin samaniya, wato Black Hole wanda yake a wuri mai nisa.


Girman ramin ya kai kilomita biliyan daya, wanda girmansa ya fi duniyarmu sau miliyan uku, wanda masana suka kira shi "dodo".

Ramin Black Hole din yana nesa daga duniya da kilomita triliyan 500, na'urar Telescope guda takwas suka dauki hoton daga duniyarmu.

An bayyana cikakkun bayanan a mujallar Astrophysical Journal.


Event Horizon Telescope (EHT) ne ya dauki hoton, manyan na'urorin hangen nesa na telescope takwas ne suka dauki hoton.

Farfesa Heino Falcle, na jami'ar Radboud dake a Netherlands, wanda ya bada shawarar binciken ne ya shaidawa BBC an samu katon ramin na black hole ne a wata samani mai suna M87.

"Abin da muke gani yafi girman sararin duniyarmu" a cewar
BBChausa.

No comments:

Post a Comment