Thursday, 4 April 2019

An yi garkuwa da kanin dan takarar gwamna a Zamfara

Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da kanin daya daga 'yan takarar Gwamnan jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal Dare a wannan makon.


An yi garkuwa da kanin Daudan a garin Gusau. Wata majiyar ta tabbatar da cewa tare da bakon sa da ya kawo masa ziyara ne aka yi awon gaba da su.

Jihar Zamfara ta zama babbar hedikwatar zubar da jinin al'umma da garkuwa da su a Nijeriya.

Allah ya ruguza aniyar azzalumai akan Zamfara. Amin.
Rariya.


No comments:

Post a Comment