Wednesday, 17 April 2019

An yi rubutun cin fuska ga Addinin Musulunci a wasu Masallatan Faransa 3


An yi rubutun cin fuska ga Addinin Musulunci a wasu Masallatan Faransa 3
A garin Rennes na kasar Faransa an yi rubutun batanci tare da nuna kyamar ga Addinin Musulunci a bangwayen wasu Masallatan Juma'a 3.


An bayyana cewar Majalisar Musulmai ta yankin Bretagne dake da alaka da Majalisar Musulmai ta Faransa za ta gabatar da korafi.
Shugaban Sashen Sanya Idanu Kan Nuna Kyama ga Musulunci na Majalisar Abdullah Zekri ya fadi cewa, sun fara aiyukan goge munanan rubutun da aka yi.
Zekri ya ja hankali da cewar a duk lokutan da za a gudanar da zabe sai an samu yawaitar kai wa Musulmai hare-hare kasar ta Faransa.
Ya ce "Tsawon shekaru 8 ina yin wannan aiki, na saba da shi. A duk lokacinda zabuka suka karato Musulmai da Musulunci na yi asara a Faransa."
A ranar 26 ga watan Mayu ne jama'ar Faransa za su zabi wakilansu da za su wakilce su a Majalisar Dokokin Tarayyar Turai.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment