Saturday, 13 April 2019

Ana jimamin shekara 12 da kisan Sheikh Jafar

A ranar Asabar ne fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Jafar Mahmud Adam ya cika shekara 12 da rasuwa.


Wadansu 'yan bindiga ne suka harbe malamin yayin da yake Sallar Asuba a ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2007 a Kano - wato a jajiberin zaben gwamnoni wanda aka yi a shekarar.

Marigayin yana daya daga cikin manyan malaman addini a bangaren mabiya Sunnah da ke da dimbin magoya baya.


Duk da cewa har yanzu jama'a na ci gaba da bayyana mutuwarsa a matsayin wani babban rashi, amma kuma har yanzu babu wani da aka kama laifin kisan malamin tukuna.

Wane ne Sheikh Jafar Adam?
An haife shi ne a ranar 12 ga watan Fabrairun shekarar 1961 a Daura jihar Katsina
Ya koma Kano don yin karatun allo yana da kimanin shekara hudu a duniya
Ya fara yin karatun addini ne a wurin mijin yayarsa
Ya haddace Al-Kur'ani a shekarar 1978
Ya fara karatun boko ne a shekarar 1990
Ya yi karatun addinin Musulunci a kasashen Saudiyya da Sudan, inda ya samu digiri na biyu.
Yana koma wa garin Maiduguri duk shekara don gudanar da tafsirin Al-Kur'ani a kowane watan azumin Ramadan
BBChausa.

No comments:

Post a Comment