Monday, 8 April 2019

Arsenal ta yi tuntube a Goodison Park.


aRSENAL
Everton ta yi nasarar doke Arsenal da ci 1-0 a wasan mako na 33 da suka kara a gasar Premier ranar Lahadi a Goodison Park.


Phil Jagielka ne ya ci kwallon tun a minti na 10 da fara tamaula, kuma hakan ne ya bai wa Eveton maki uku rigis a karawar.
Wasa na uku a jere da Everton ta yi nasara kenan a gasar cin Kofin Premier, inda hakan ya sa ta hada maki 46 tana ta tara a kan teburi.
Ita kuwa Arsenal wadda take fatan kammala wasannin bana cikin 'yan hudun farko tana ta hudun da maki 63.
Arsenal ce kungiyar da kwallo ya shiga ragarta a wasannin da ta buga ba a gidanta ba kawo yanzu.
Rashin nasarar da Arsenal ta yi ya sa ba za ta koma ta uku a kan teburi ba, bayan karawar mako na 33, inda Tottenham ce ta ci gaba da zama a gurbin.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment