Saturday, 13 April 2019

Atiku ba dan Najeriya bane>>APC ta gayawa kotun sauraren karar zabe

Jam'iyya me mulki ta APC ta gayawa kotun saurararen karar zaben shugaban kasa dake da zama a babban birnin tarayya, Abuja cewa dan takarar shugaban kasar karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ba haifaffan Najeri bane, dan asalin kasar Kamarune dan haka baima cancanta ya tsaya takarar shugaban kasa ba.APC ta yi wannan maganane a matsayin martani ga korafe-korafen da dan takarar ya shigar gaban kotun inda yayi ikirarin cewa shine ya lashe zaben shugaban kasar daya gabata dan haka kotun kodai ta ayyanashi a matsayin zababben shugaban kasa ko kuma ta tilastawa hukumar zabe me zaman kanta, INEC sake yin wani sahihin zaben da za'ayi bisa doka da oda.

A nata martanin, APC ta kara da cewa, sakamakon zaben da INEC ta fitarne kawai sahihin sakamakon zabe da ya kamata a amince dashi kuma ikirarin PDP na cewa shugaba Buhari baida cikakkun takardun makaranta da za zasu bashi damar tsayawa zabe wannan tsohon zancene da tun tuni ya kamata PDP ta yi korafi akanshi tun kamin zabe amma ba yanzu da aka kammala zabe na dan haka kotun bata da hurumin sauraren wannan korafin.

Andai tashi daga zaman kotun ba tare da bayyana ranar da za'a sakeci gaba da zaman sauraren karar ba.

No comments:

Post a Comment